Yaya Toure ne zakaran kwallon Afrika na 2011

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaya Toure ya taka rawa sosai a Manchester City

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika Caf, ta bayyana dan wasan Ivory Coast Yaya Toure a matsayin zakaran dan wasan kwallon kafa na Afrika na 2011.

Dan wasan na Ivory Coast da Manchester City ya doke Seydou Keita, na Mali da Barcelona, da dan Ghana Andre Ayew, wanda ke taka leda a kulob din Olympique Marseille.

Kocin kwallon kafa na kasashen Afrika ne suka zabi Toure, mai shekaru 28 da haihuwa.

"Wannan ita ce kyauta mafi girma da zan samu a rayuwa ta," a cewar Toure, wanda ya taimaka wa Man City ta hau saman gasar Premier ta Ingila.

Shi ne ya kuma zira kwallo dayan da ta baiwa City nasara a wasan da ta doke Stoke domin lashe gasar cin kofin FA a watan Mayu.

Toure wanda ke cike da farin ciki ya ce yana alfahari da kyautar da ya samu a wannan 'ranar ta musamman'.

'Wacce na da matukar muhimmanci'

Kuma yana fatan kyautar za ta karfafa wa Ivory Coast gwiwa wajen lashe gasar cin kofin kasashen Afrika da za a yi badi.

"Nan da watanni kadan, za mu fuskanci gasar cin kofin kasashen Afrika wacce na da matukar muhimmanci ga ni da kuma kasata," a cewarsa.

Nasarar ta Toure daya ce daga cikin wacce Ivory Coast ta samu a daren - sun kuma samu alkalin wasan da ya fi kowanne nuna bajinta a 2011, wanda shi ne Noumandiez Doue.

Dan wasan Tottenham Souleyman Coulibaly ne ya lashe kyautar dan wasa mai tasowa.

Yayin da Oussama Darragi Esperance shi aka zaba gwarzon dan kwallon Afrika - wanda ke taka leda a nahiyar ta Afrika.

Kocin Niger Harouna Doula shi aka zaba kocin da ya fi kowanne taka rawar gani a nahiyar Afrika.

Sai tawagar kwallon Botswana wacce za ta halarci gasar cin kofin Afrika a karon farko - ita ce tawagar da ta fi kowacce a bana.

An kuma zabi Kamaru a matsayin tawagar kwallon mata da ta fi kowacce a Afrika a 2011.

Yayin da aka zabi 'yar kwallon Najeriya Perpetual Nkwoche a matsayin zakarar kwallon Afrika ta 2011.