An fara bincike kan wariyar launin fata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan a lokacin gasar French League

Hukumar gasar 'League' ta Faransa ta fara gudanar da bincike game da zargin wariyar launin fata da dan wasa, Kamel Chafni, ya ce mataimakin alkalin wasa ya yi masa a wasan da Auxerre ta ci Brest daya ranar Asabar.

Chafni ya yi ikirarin cewa mataimakin alkalin wasan, Johann Perruaux, ya ce masa '' tafi daga nan, Balarabe'', da zummar muzanta shi.

An dai kori dan wasan daga fili bayan da ya yi ta kalamai don jawo hankalin alkalin wasa game da zargin muzantawar da aka yi masa.

Sai dai ranar Lahadi, shugaban hukumar gasar League ta Faransa, Frederic Thiriez, ya bayar da umarnin gudanar da bincike game da batun, '' domin bayyana gaskiya ko akasin haka game da zargin cikin gaggawa''.

Thiriez ya dauki matakin ne bayan ya tattauna da shugaban Auxerre, Gerard Bourgoin, da shugaban da ke kula da alkakan wasa a gasar, Marc Batta, da kuma alkalin wasan, Tony Chapron.