Bani da wani wa'adi, in ji kocin Blackburn

steve kean Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption steve kean

Kocin klub din Blackburn Rovers Steve Kean ya bayyana cewa, ya gana da wadanda suka mallaki klub din a ranar Lahadi, inda ya hakikance cewa, aikinsa ba ya fuskantar wata barazana.

Da aka tambaye shi, ko daya daga cikin wadanda suka mallaki klub din sun ba shi wa'adi kafin wasan da klub din zai doka da klub din Bolton a ranar Talata, sai Kean ya ce, 'ko kadan, babu wanda ya ba ni wa'adi'.

Ya ce, sun tattauna tare da shi na tsawon mintuna arbain da biyar, kuma a cewarsa ganawar ta yi fa'ida. Ya ce su na hankoron zuwan lokacin musayar yan wasa.

Kean dai na fuskantar matsin lamba sosai, bayan da klub din sa ya sha kashi a hannun West Brom a ranar Asabar da ta gabata.

Wasu jaridu sun bada rahotanni a yau Litinin cewa, tsohon dan wasan gaba na klub din na Blackburn Alan Shearer da tsohon kocin klub din Portsmouth wato Avram Grant ka iya karbar jagorancin klub din na Rovers. Ita kuwa jaridar Lancashire Telegraph ta yi kira ne ga Kean da yayi murabus a shafinta na farko.

To amma Kean ya tsaya kan bakarsa ta cewa, zai jagoranci klub din kamar yadda ya saba a wasan da za su doka da Bolton a ranar Talata.

Ita dai klub din Blackburn na kan gaba ne da maki guda da kuma wasa daya akan abokiyar karawar ta, wadda ke can kasa a wasan Premier, kuma Kean ya hakikance cewa babu wata matsi da za ta sa klub din sa ya gaza kai gaci, inda yake fuskantar fita daga gasar Premier.