John Terry ya yi rauni a idon sawunsa

John Terry Hakkin mallakar hoto AP
Image caption John Terry

Ana sa ran Kyaptin din klub din Chelsea John Terry zai samu karfin doka wasan da za su buga da klub din Tottenham a ranar Alhamis mai zuwa, duk da raunin da ya samu a idon sawunsa lokacin da suke wasan motsa jiki.

Sai da aka dauke shi daga filin wasan, bayanda ya samu raunin a kafar sa ta dama.

Klub ya rubuta a shafin sa na sada zumunta na Twitter cewa, raunin da Terry ya samu a lokacin da ya tare kwallo, ba zai hana shi yin wasan da za su yi a ranar Alhamis ba.