Muna bukatar karin 'yan wasa- Warnock

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tambarin Queens Park Rangers

Kocin Queens Park Rangers, Neil Warnock, ya ce kulab din na bukatar karin 'yan wasa guda biyu ko uku bayan da Mancheter United ta ci su biyu ba ko daya a wasana da suka buga a karshen mako.

Mr Warnock, ya ce ya gamsu da rawar da kulab din sa ya taka, yana mai cewa: '' wasu lokutan 'yan wasa na na yin zarra matuka''.

Kulab din dai shi ne na goma sha biyar a kan teburin gasar Premier ta Ingila.

Amma duk da haka kocin ya ce idan suka sayi sababbin 'yan wasa, za su baiwa-mara-da-kunya a wasannin da za su buga a nan gaba.