Babu inda Tevez zai je, in ji Mancini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Carlos Tevez

Manajan klub din Manchester City, Roberto Mancini ya sake jaddada matsayar sa cewa dan wasan gaba na klub din Carlos Tevez ba zai koma AC Milan ba a watan Janairu.

Mataimakin shugaban klub din Milan, Adriano Galliani ya ce zai tattauna tare da mahukuntan City a ranar Alhamis mai zuwa, bisa yiwuwar komawar dan wasan mai shekaru 27 a duniya zuwa klub din na Milan.

Mancini ya ce, fata na shi ne mu samar wa kan mu da Carlos makoma mai kyau.

Ya ce, ita kan ta Milan ta san cewa ba za mu ba da shi a matsayin aro ba, to amma idan siyan sa su ke son su yi, to kofa a bude take.

A baya dai, Milan ta ba da tayin siyan dan asalin kasar Argentinan a kan dala million 19 da digo ukku, amma shugabannin wasan Premier su ka yi fatali da tayin.