Wasan kurket zai ci gaba a Pakistan a 2012

Yan wasan kurket na Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yan wasan kurket na Pakistan

Hukumar wasan Kurket na kasar Pakistan PCB, ta ce, ta na sa ran a shekarar 2012, kasar za ta ci gaba da karbar bakuncin kasashen duniya a wasannin kasa da kasa.

Pakistan dai ta na buga dukkanin wasannin ta ne a ketare, tun bayan da masu ta da kayar baya suka kai hari kan yan wasan kasar Sri Lanka a Lahore a shekarar 2009.

To sai dai shugaban hukumar wasan Kurket din, Zaka Ashraf, ya gayyaci kasar Bangaladesh da su je Pakistan din don ziyarar gane wa idon su yanayin kasar.

Ashraf ya ce, ya na da kwarin gwiwar sake farfadowar wasan kurket a Pakistan.

Hadaddiyar Daular Larabawa ce za ta kasance a matsayin gida ga Pakistan a wasan da za su yi da Ingila a sabuwar shekara mai kamawa.