Ta na kasa ta na dabo ga kocin yan wasan Senegal

Amara Traore Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amara Traore

Mai horar da yan wasan kasar Senegal, Amara Traore, ya kasa sabunta kwangilar sa ta horar da yan wasan kasar, ana saura wata guda a fara gasar cin kofin Afirka.

Tattaunawar sabunta kwangilar ta sa, ta ci tura, bayan karewar ta a ranar 15 ga watan Decebar nan.

Hukumar kwallon kafar Senegal tare da shi kan sa sun so sabunta kwantaragin na sa, bayan da ya cimma kudurin da aka debar masa na kai yan wasan kasar zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a kasashen Gabon da Equatorial Guinea.

To sai dai tattaunawar ta ci tura, bayan da Traore ya nemi a kara ma sa kudi.

Shi dai Traore dan shekaru 46 a duniya, ya nemi tsawaita waadin sa ne da shekaru biyu da kuma CFA million 12 kwatankwacin dala dubu ashirin da ukku da dari takwas a matsayin albashin wata-wata, albashin da ministan wasannin kasar ya ki amincewa da shi.