United ta koka akan tikitin wasanta da City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchster United, Sir Alex Ferguson

Manchester United ta yi korafi akan yadda hukumar kwallon kafa ta Ingila ta warewa magoya bayan City tikiti mafi yawa a gasar wasan cin kofin FA na zagaye na uku da za su buga a watan Janairu.

A karkashin dokar hukumar kwallon Ingila dai, United ce ya kamata ta samu tikitin mutane 7,100 a filin wasan Mancehster City.

Sai dai City ta bayar da tikiti 5,500 inda ta ce ta yi hakan ne saboda dalilan tsaro a yayin gudanar da wasan. Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta baiwa United gurbi na musamman saboda girman filin wasanta, watau Old Trafford wanda ke da gurabe 76,000.

United na so ne a basu cikakkun gurabe yadda magoya bayansu za su samu damar yabonsu a lokacin gudanar da wasan, wadan za a fara ranar takwas ga watan Janairu.