Manajan Chelsea ya bayyana shaawarsa ta siyan Cahill

Andre Villas-Boas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Andre Villas-Boas ya bayyana shaawarsa ta siyan dan wasan baya na klub din Bolton Gary Cahill.

Kwantaragin Cahill dan shekaru 26 a duniya, za ta kare a karshen kakar shekara da klub din Bolton, kuma da alamu su amince da bayar da shi idan kofar hakan ta bude.

Klub din Arsenal ta ba da tayin ta na siyan Cahill a watan Agustan da ta gabata, amma Bolton ta ki, saidai a yanzu Villas Boas ya yunkuro.

Ita dai Bolton ta zargi Arsenal ce da yi mata tayin wulakanci na siyan Cahill, zarginda kocin Asenal Arsene Wenger ya musanta da kakkausar murya.