FA ta hukunta Luis Suarez

Image caption Suarez

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, wato FA, ta dakatar da dan wasan Liverpool, Luis Suarez, daga buga wasanni takwas a gasar Premier bayan da ta same shi da laifin nuna wariyar launin fata.

Hukumar ta kuma ci tararsa fam 40,000.

Suarez ya nunawa dan wasan Manchester United, Patrice Evra, da dan yatsa, abin da ke nufin zagi da wariyar launin fata a lokacin da kungiyoyin biyu suka buga wasa a watan Oktoba.

Suarez, wanda ya musanta aikata ba dai-dai ba, na da kwanaki goma sha hudu domin ya daukaka kara.

A baya ma an zarge shi da yin kalamin da ke nuna wariyar launin fata.