Arsenal ta dage wasan ta da Wolves

Filin wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasan Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta dage wasan da za ta yi da klub din Wolves da kwana guda, zuwa 27 ga watan December.

Arsenal dai ta yanke wannan shawarar ce a sabili da yajin aikin da maaikatan jiragen kasa na London suka shirya yi, kwana guda bayan ranar Kirismeti.

Sanarwar da Arsenal ta fitar na cewa, "babban abin damuwar mu shi ne, tsaron lafiyar magoya bayan mu, da ma duk wanda ke shirin kallon wasan na bayan ranar Kirismeti.

Ita kuwa klub din Chelsea, ta ba da tabbacin cewa wasan ta na bayan ranar Kirismeti da Fulham na nan daram.