Suarez zai daukaka kara kan haramcin wasanni 8

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Luis Suarez

Dan wasan gaba na klub din Liverpool Luis Suarez zai daukaka kara game da hukuncin da hukumar kwallon kafa ta FA ta gabatar akan sa, bisa kalaman batanci da ake zargin sa da yi wa Patrice Evra.

Lauyan sa Alejandro Balbi ne ya ba da wannan sanarwa kuma ya ce dan wasan ya na da kwarin gwiwar cewa za a sauya hukuncin.

Hukumar FA dai ta yanke wa Suarez ne haramcin buga wasanni takwas da kuma tarar pan dubu arbain, bisa zargin sa da yin mafani da da kalaman banbanci launin fata a kan Evra dan wasan baya na Manchester United.

Suarez dai wanda ya sha musanta zargin, na da kwanaki 14 don ya daukaka kara kan matakin. Idan ya yi haka akwai yiwuwar a tsawaita haramcin.