Suarez ya amince da aikata ba daidai ba

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Luis Suarez

Dan wasan Liverpool, Luis Suarez, ya amince da nuna wa dan wasan Manchester United, Patrice Evra, wariyar launin fata a lokacin da aka buga wasa tsakanin kulab-kulab din.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da shi daga buga gasar Premier sau daya, sannan ta ci tararsa fam dubu ashirin.

Ta kuma gargade shi kan ya daina nuna wariyar launin fata.

A yanzu dai Suarez ba zai buga wasan Premier wanda za a yi ranar Juma'a ba, inda kulab dinsa zai kara da Newcastle United.

A kwanan baya ne dai hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da Suarez daga buga wasa har sau takwas sakamakon daga dan yatsan da ya yi wa Evra lokacin da Manchester United ta doke kulab din sa da ci daya mai ban haushi.