Mun samu kwarin gwiwa, in ji Kean

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steve Kean

Kocin Blackburn Rovers, Steve Kean, ya ce sun samu kwarin gwiwa dangane da matakin da suke a gasar Premier daga wajen koca-kocai na wasu kulab-kulab din.

Kean, wanda kulab din sa ke neman maki biyar domin hayewa tudun-mun-tsira a gasar Premier, ya ce ya yi ganawa mai armashi da kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, abin da ya kara masa kwarin gwiwa.

Ya ce:"Ba zan bayyana abin da muka tattauna a kai ba, amma tattaunawar ta yi armashi.Yadda shi( Ferguson) ya kira ni ta wayar salula, sannan ya nuna mini goyon baya, ya bayyana irin matsayinsa na mutum mai kirki.Na ji dadi da hakan''.

Kean, wanda ya ce ya samu sakonnin karfafa gwiwa daga koca-kocai kamarsu Harry Redknapp, da David Moyes da Alan Pardew, ya yadda cewa Ferguson ba zai yi musu da wasa ba, a yayin da kulab din sa zai fafata da Manchester United a wasan da za su yi ranar Asabar.