Wasu dalilai sun sa Beckham ya fasa zuwa PSG

David Beckham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Beckham

Rahotanni daga Faransa sun nuna cewa David Beckham ya yanke shawarar ba zai koma kulob din Paris Saint-Germain ba saboda wasu dalilai na iyali.

A baya dai an alakanta tsohon kyaftin din na Ingila da yunkurin komawa kulob din na Faransa mallakar 'yan kasar Qatar, amma kuma yanzu zai tsawaita zamansa a Amurka tare da kulob din Los Angeles Galaxy.

Daraktan wasannin na Paris Saint-Germain, Leonardo, ya shaidawa jaridar L'Equipe cewa "Abin takaici, yarjejeniyar ta tsaya".

Ya kuma kara da cewa, "bukatun iyalinsa, da kuma fatan da Beckham ke da shi cewa ba zai sauya yanayin rayuwarsa ba sun yi tasiri sosai".