Aston Villa na neman aron Robbie Keane

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Robbie Keane

Aston Villa ta nuna sha'awar siyan dan wasan Los Angeles Galaxy Robbie Keane na wucin gadi na tsawon watanni biyu.

Amma a yanzu haka, Keane na horo ne da tsohuwar kungiyarshi ta Spurs har sai ranar 21 ga watan Junairu.

Kocin Villa, Alex McLeish dai ya nuna sha'awarshi na siyan dan wasan da dadewa.

A kakar wasan bara, sai da kocin ya kusan siyan dan wasan a lokacin da ya kae horon kungiyar Birmingham.

Keane dai yana so ya ci gaba da taka leda domin ya kara kwazo da himma kadin a fara gasar cin kofin nahiyar Turai.

A yanzu haka dai ana hutun a gasar Major League Soccer ta Amurka kuma za a dawo gasar ne a watan Maris.