Chelsea za ta iya lashe gasar Premier- Lampard

Image caption Dan wasan Chelsea, Frank Lampard

Dan wasan Chelsea, Frank Lampard ya ce Chelsea za ta ci gaba da fafutukar lashe gasar Premier kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba.

A makon da ya gabata, kocin kungiyar, Andre Villas-Boas bayan kunnen dokin da kungiyar ta buga da Fulham ya ce sun fidda rai a kan lashe gasar.

Amma bayan nasarar da kungiyar ta samu akan Wolves a ranar Litinin, Lampard ya ce kungiyar za ta ci gaba da fafutukar lashe gasar, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba.

"Muna da kyau, kuma a ganina ya kamata muna kan gaba." In ji Lampard.

A yanzu haka dai, Chelsea ce ta hudu a kan tebur a gasar ta Premier.