Arsene Wenger ya fusata da alkalin wasa

Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya alakanta rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a wasan ta da Fulham ga alkalin wasa Lee Probertg.

Arsenal dai ta sha kashi ne a tattakin da ta kai Fulham da ci biyu da daya.

Arsenal ta zura kwallon farko ne tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma sai ana sauran minti biyar a kammala wasan Fulham ta fanshe sannan kuma ana karin lokaci ta zura ta biyu.

Wenger dai ya nuna rashin jin dadinsa ga sallamar da aka yiwa dan wasan bayansa Johan Djourou bayan an nuna masa katin gargadi na biyu.

"A gaskiya a ra'ayi na alkalin wasa na da hannu a dokemu da aka yi." In ji Wenger.

Wenger dai ya ce bai kamata a nunawa Djourou katin gargadi na farko ba, domin bai yi laifi mai tsauri ba.

A yanzu haka dai, Arsenal ce ta biyar a tebur a yayinda take biye da Chelsea, wadda maki biyu ne tsakaninsu.