Manchester City ta fi karfin Liverpool

aguero Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sergio Aguero na Man City

Manchester City ta farfado daga kashin data sha a wajen Sunderland, inda ta kara tazarar maki uku a saman tebur bayan ta lallasa Liverpool daci uku da nema a wasan gasar premier da suka buga.

Tawagar Roberto Mancini ta fuskanci kalubale sakamakon rashin nasararta kwanaki biyun da suka wuce, amma kuma bisa dukkan alamu City ta nunawa Liverpool cewar ruwa ba tsaran kwando bane kuma ta shirya bada mamaki a gasar premier ta bana a Ingila.

Sergio Aguero ne ya ciwa City kwallon farko kafin Yaya Toure ya ci kwallo na biyu sai kuma James Milner ya zira ta uku a bugun fenariti.

A lokacin wasan dai Lius Suarez na Liverpool bai buga saboda dakatar dashi da akayi sakamakon kalaman batanci daya yiwa Patrice Evra na Manchester United.

Tsaikon da Manchester City ta samu a wasan dai shine korar da aka yiwa Gareth Barry abinda ke nufin cewar ba zai buga wasan na zagaye na uku ba a gasar kofin FA tsakaninsu da Manchester United.

Sakamakon sauran karawar da aka yi a daren Talata a Ingila:

* Tottenham 1 - 0 West Brom * Wigan 1- 4 Sunderland

Karin bayani