Dalglish ya kara kare Suarez akan batun Evra

suarez Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Lius Suarez da Patrice Evra

Kenny Dalglish ya kare matakin Liverpool akan batun Luis Suarez inda yace ba a bayyana cikakken bayanai ba akan binciken.

Liverpool ta ce ba zata kalubalanci dakatarwar wasanni takwas da aka yi Suarez akan kalaman wariyar launin fata akan dan wasan Manchester United Patrice Evra.

Kulob din da dan kwallon sun tsaya kaida fata akan batun na Suarez.

Dalglish yace"bana tunanin cewar suna yin bincike yadda ya kamata, amma dai abun takaici ne".

Wani kwamitin bincike da hukumar kwallon Ingila ta kafa ta yanke hukuncin cewar, Suarez mai shekaru 24, ya yiwa Evra kalama wariyar launin fata a wasa tsakanin Liverpool da Manchester United a Oktoba.

Wasannin da za ayi banda Suarez:

* 3 Jan: Man City (Premier League) * 6 Jan: Oldham (FA Cup R3) * 11 Jan: Man City (League Cup) * 14 Jan: Stoke (Premier League) * 21 Jan: Bolton (Premier League) * 25 Jan: Man City (League Cup) * 28 Jan: FA Cup R4 (idan Liverpool ta doke Oldham) * 31 Jan: Wolves (Premier League) * 6 Feb: Tottenham (Premier League)

Karin bayani