Steve McClaren ya kara komawa FC Twente

Image caption Steve McClaren

Tsohon kocin Ingila Steve McClaren ya koma aikinsa na da a kungiyar FC Twente.

McClaren, mai shekarun haihuwa 50 ya hori kungiyar na tsawon kakar wasanni biyu a yayinda ya lashe gasar Eredivisie a shekarar 2009-10, amma sai ya ajiye aikinsa ya koma kungiyar Wolfsburg ta kasar Jamus.

An sallame shi daga mukaminsa a watan Fabrairun shekarar 2011 sannan ya koma Nottingham Forest inda ya yi aikin na tsawon kwanaki 112 kafin ya ajiye a watan Okutoba.

FC Twente dai ta sallami tsohon mai horadda da ita Co Adriaanse a ranar Talata.

Adriaanse, ya karfi aiki horon kungiyar ne a farkon kakar wasan bara.