Pardew ya yaba da kokarin Demba Ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan Senegal dake kungiyar Newcastle, Demba Ba

Kocin Newcastle, Alan Pardew ya jinjinawa dan wasan Senegal dake kungiyar wato Demba Ba, saboda yadda yake haskakawa.

Demba Ba ya zura kwallonsa ta 15 ne a wasan da Newcastle to doke Manchester United da ci uku da nema a daren ranar Laraba.

Wasan da dan wasan ya buga shine na karshe a kungiyar kafin ya wuce gasar cin kofin Afrika.

"Duk inda na sa shi yana haskakawa, ya buga a bangarori har uku a filin wasa, kuma a duka ya nuna kwazon sa." In ji Pardew.