Fecafoot zata duba dakatarwar data yiwa Eto'o

etoo
Image caption Samuel Eto'o Fils na Kamaru

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Kamaru-Fecafoot a ranar Juma'a zata tattauna batun dakatarwar wasanni goma sha biyar data yiwa Samuel Eto'o.

An dauki hukuncin dakatar da Eto'o ne bayan da ya jagoranci yajin aiki na 'yan wasan Indomitable Lions akan batun kudaden alawus.

Wannan hukuncin ya fuskanci suka a fadin kasar, inda jama'a ke yin kira a maidoda Eto'o.

Koda yake dai batun Eto'o baya cikin abubuwa da aka tsara za a tattauna lokacin taron, amma dai mambobin kwamitin zasu iya tayarda maganar don ayi mahawara akanta.

Jami'an Fecafoot na fuskantar matsin lamba akan batun, inda wasu rahotanni ke cewar shugaban kasar Paul Biya ya shiga cikin batun, duk da cewar kakakin Fecafoot ya karyata.

Eto'o bai kalubalanci dakatarwar ba, abinda zai hanashi taka leda har sai lokacin gasar kofin kwallon duniya a Brazil a shekara ta 2014.

Karin bayani