Ahmed Musa ya koma CSKA Moscow daga VVV Venlo

ahmed musa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Musa

Kungiyar CSKA Moscow ta Rasha ta amince ta kulla yarjejeniya da dan Najeriya wanda ke taka leda a kungiyar VVV Venlo ta Netherlands Ahmed Musa.

Dan wasan mai shekaru goma sha tara za a gwada lafiyarsa a ranar Litinin kafin ya sanya hannu a kwangilar shekaru hudu da rabi akan kudaden da ba a san yawansu.

Musa ya shaidawa BBC cewar "an kamalla yarjejeniya tsakanin Venlo da CSKA".

Wasu kungiyoyi daga Jamus da Ukraine da Spain da kuma Turkiya amma kuma CSKA ce kawai ta biyan kudin da ake bukata."

Musa ya hade da dan Ivory Coast Seydou Doumbia da kuma Sekou Oliseh na Liberia a CSKA.

Kungiyoyin da Musa ya bugawa:

* 2008-09: JUTH (Najeriya) * 2009 -10: Kano Pillars (Najeriya) * 2010 -12: VVV Venlo (Netherlands) * 2012 - : CSKA Moscow (Rasha)