Scholes ya dawo tamaula bayan ritayarsa

scholes Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Paul Scholes

Paul Scholes ya dawo daga ritayar da yayi inda ya koma bugawa Manchester United kwallo har zuwa karshen kakar wasan bana.

Tsohon dan kwallon tsakiya a Ingila din mai shekaru talatin bakwai da farko ya yi ritaya ne a karshen kakar wasan data wuce, inda ya koma horarwa a United.

Amma sai aka shawo kansa ya koma fili saboda matsalar raunin da United ke fuskanta.

Scholes yace "Na ji dadin yadda kocina yake ganin cewar zan bada gudunmuwa a tawagar".

Dan wasan a duk tsawon rayuwarsa ya taka leda a Old Trafford inda ya soma bugawa babbar tawagar a shekarar 1994.

Scholes ya lashe kofinan gasar Premier goma tare da na gasar zakarun Turai.

Karin bayani