'Yan wasan Botswana sun janye yajin aiki

bostwana Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Botswana da kocinsu

'Yan wasan kwallon kafa na kasar Botswana sun fasa yin yajin aikin da suka shirya yi bayan da aka bayyana musu cewar babu kudin garabasa da za a basu lokacin gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika.

Shugaban kasar ya yi kira ga 'yan kwallon su saka kishin kasa a gaba fiye da san kansu.

Da farko dai 'yan wasan sun ki yin horo don shiryawa karawarsu da Zimbabwe a wasan sada zumunci.

Kocin Botswana Stanley Tshosane ya saka kyaftin dinsa wanda ke fama da rauni wato Mompathi Thuma a cikin jerin tawagarsa da zata buga gasar.

Tawagar na bukatar a bata dalar Amurka dubu goma sha uku ga kowanne dan kwallo da zai tafi gasar sannan kuma a basu garabasa idan har suka yi nisa a gasar.

Amma dai hukumar kwallon Botswana ta ce ba zata kara wasu karin kudade ba da 'yan wasan ke bukata.