Man City ta kalubalanci jan katin Kompany

kompany Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vincent Kompany

Manchester City na kalubalantar jan katin da aka baiwa kyaftin dinta Vincent Kompany lokacin wasansu da Manchester United a gasar cin kofin FA na Ingila.

Dan wasan na kasar Belgium ya fuskanci fushin alkalin wasa Chris Foy saboda irin yadda ya kaiwa dan wasan United, Nani hari.

Kulob din ya ce ya kamata a sake duba lamarin, a yayinda hukumar dake kula da kwallon kafa a Ingila wato FA ta bayyana cewar a ranar Talata.

Idan har basu samu nasara ba akan kalubalantar da City ta yi ba, tabbas kulob din zai buga wasanni hudu babu kyaftin din.

Manchester City a halin yanzu tana kewar Kolo Toure da Yaya Toure wadanda suka tafi hutu saboda gasar cin kofin Afrika da zasu bugawa Ivory Coast.