Messi ne gwazon dan kwallon duniya na 2011

messi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lionel Messi

Lionel Messi ya samu kyautar Fifa Ballon d'Or wato kyautar gwarzon dan kwallon duniya a wani buki da aka yi a Zurich, Switzerland.

Ya kasance dan kwallo na hudu a tarihi da ya lashe wannan kyautar sau uku.

Dan Argentinan mai shekaru 24 ya shiga gaban dan Real Madrid Cristiano Ronaldo da kuma Xavi na Barcelona.

Kocin Barcelona Pep Guardiola shine ya samu kyautar kocin da yafi kowanne a duniya.

A bangaren mata kuwa 'yar Japan Homare Sawa itace zakara a duniya sai kuma dan wasan Brazil Neymar ya samu kyautar wanda kwallonshi ta fi ta kowa a duniya a bara.

Karin bayani