Ballon d'Or: Messi na gabda kafa tarihi

messi, xavi da ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo da Xavi da Messi

Lionel Messi na gabda kafa tarihi a matsayin dan kwallo na uku a duniya da zai samu kyautar gwarzon dan kwallo na FIFA , a yayinda ake shirin bada kyautar a ranar Litinin a birnin Zurich.

Mutane uku ne ke takarar hadda Cristiano Ronaldo da Xavi.

Messi mai shekaru 24 shine ya samu kyautar a shekara ta 2009 da 2010.

Zinedine Zidane na Faransa da kuma dan Brazil Ronaldo sune kadai suka taba samun kyautar har sau uku.

Dan wasan Barcelona Gerrard Pique ya bayyana Messi a matsayin wanda yafi kowane dan kwallo a duniya.

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney yana takara akan zira kwallonda yafi kowanne.

Kocin Barcelona Pep Guardiola da Jose Mourinho na Real Madrid da kuma Sir Alex Ferguson na Manchester United suna takarar neman samun kyautar kocin da yafi kowanne.

Manema labarai da masu horadda 'yan kwallo da kuma kyaftin na kasashen ne ke zaben wanda za a baiwa kyautar ta gwarzon dan kwallon duniya.

Karin bayani