Henry ya nuna gawurtarsa a Arsenal

henry Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Thiery Henry

Arsene Wenger ya ce Thierry Henry ya kara nuna matsayinsa na gawurta a Arsenal bayan ya zira kwallon data baiwa kulob din nasara akan Leeds a wasan cin kofin FA.

Dan kwallon mai shekaru talatin da hudu yana matsayin aro na watanni biyu a Arsenal daga kungiyar New York Red Bulls.

A shekara ta 2007 ne Henry ya bar Arsenal ya koma Barcelona, kuma mintuna goma da shigowar fili a wasan Arsenal da Leeds sai ya zira kwallo, nasarar data sanya Gunners din zasu fuskanci Aston Villa a zagaye na hudu a gasar kofin FA.

Henry dai ya nuna cewar shi kwararre ne kuma Wenger ya ce "Shi dama babban dan wasa ne kuma ya kara tabbatar da haka".

Henry ya zirawa Arsenal kwallaye 227 kuma a halin yanzu ya kulla yarjejeniyar makwanni shida da rabi tare da kulob din.

Karin bayani