Ivory Coast ta bayyana sunayen 'yan wasa 23

ivorycoast football Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Didier Drogba

Kocin Ivory Coast Francois Zahoui ya bayyana jerin 'yan wasa ashirin da uku da zasu wakilci kasar a gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika.

Sai dai an fidda sunaye 'yan kwallo biyu wato Marco Taddei Ne da kuma Ibrahim Kone daga cikin tawagar.

Duka 'yan wasan 23 suna buga kwallo a wajen Ivory Coast.

Cikakkiyar tawagar:

Masu tsaron gida: Barry Boubacar (Lokeren, Belgium), Gerrard Gnanahouan (Avranches, France), Daniel Yeboah (Dijon, France)

Masu buga baya: Siake Tiene (Paris St Germain, France), Arthur Boka (Stuttgart, Germany), Benjamin Angoua Brou (Valenciennes, France), Igor Lolo (FC Kuban Krasnodar, Russia), Didier Zokora (Trabzonspor, Turkey), Emmanuel Eboue (Galatasaray, Turkey), Kolo Toure (Manchester City, England), Souleymane Bamba (Leicester City, England)

Masu buga tsakiya: Kafoumba Coulibaly (Nice, France), Jean-Jacques Gosso Gosso (Orduspor, Turkey), Didier Ya Konan (Hannover, Germany), Cheick Tiote (Newcastle United, England), Max Gradel (St Etienne, France), Yaya Toure (Manchester City, England)

Masu buga gaba: Gervinho (Arsenal, England), Seydou Doumbia (CSKA Moscow, Russia), Didier Drogba (Chelsea, England), Salomon Kalou (Chelsea, England), Wilfried Boni (Vitesse Arnhem, Netherlands), Abdul Kader Keita (Al Sadd, Qatar)