Afuwar da Suarez ya nema, nada mahimanci

mancini Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce akwai mahimancin gaske sosai akan Luis Suarez ya nemi afuwa bayanda aka sameshi da laifin yiwa Patrice Evra kalaman wariyar launin fata.

A yayinda City ke shirin fuskantar Liverpool a wasan zagayen kusada karshe na gasar kofin Carling, Mancini ya ce Suarez yayi kuskure amma kuma bai kamata a dunga kallonshi a matsayin mai nuna bambamcin launin fata ba.

Mancini ya kara da cewar "ba zai yiwu ace mutum baya kuskure ba".

Yace"Komai na iya faruwa idan mutum bai cika tunani ba".

An dakatar da Suarez na wasanni takwas ne bayanda da hukumar bincike mai zaman kanta a Ingila ya same shi da laifi.

Kuma Suarez din bai daukaka karar ba sannan sai ya nemi afuwa a ranar biyar ga watan Junairu.