Gerarrd ya amince da kwangilar dadewa a Liverpool

gerard Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Steven Gerrard

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya sanya hannu a kwangilar cigaba da kasancewa da kulob din na lokaci mai tsawo.

Gerrard wanda ya soma taka a Anfield tun yana karamin yaro , inda ya soma bugawa babban tim din a watan Nuwambar 1998.

A jawabinsa bayan sanya hannu a kwangilar ya ce "Na yi matukar farin ciki. Wannan babbar rana ce ga ni da iyalai na".

Gerrard ya amince da kwangilar ne kwana guda bayan da ya zira kwallo a wasan da suka doke Manchester City a gasar kofin Carling.

Kawo yanzu dai Gerrard ya zira kwallaye uku kenan a kakar wasa ta bana tun bayan da yayi jinyar watanni biyu sakamakon rauni a idon sawunsa.

Dan wasan Ingila ya bugawa Liverpool wasanni 566 tun soma taka leda a Anfield.

Har wa yau ya bugawa Ingila wasanni 89 a yayinda ya amince da karbar matsayin jakadan kulob din idan yayi ritaya.