An gwada lafiyar Cahill a Chelsea

cahill
Image caption Gary Cahill

Dan kwallon bayan Bolton Gary Cahill na gabda komawa Chelsea bayan da aka gwada lafiyarsa.

Ana saran a ranar Litinin za a gabatar Cahill a matsayin dan wasan Chelsea bayan ya kamalla gwaje gwaje a ranar Asabar.

Bisa dukkan alamu Cahill zai iya bugawa Chelsea a ranar Asabar mai zuwa tsakaninta da Norwich.

Yana cikin 'yan kallo a Stamford Bridge a lokacin wasan Chelsea da Sunderland a ranar Asabar da rana.

Rahotanni sun nuna cewar kwangilar ta kai ta fan miliyon bakwai akan Cahill mai shekaru ashirin da shida.