Chelsea ta amince da tayin QPR akan Alex

alex
Image caption Alex na Brazil

Kungiyar Queens Park Rangers ta amince ta sayi dan wasan Chelsea Alex na Brazil.

Dan wasan mai shekaru 29 ya amince da ya koma QPR.

Chelsea ta ki amincewa da tayin farko akansa amma kuma tana bukatar ta samu wasu kudade akan dan wasan kafin ya tafi saboda sun ce ba zai dunga samun bugawa ba a Stamford Bridge.

A mako mai zuwa ne Alex zai tattauna da QPR akan kwangilar.

Alex ya koma Chelsea ne daga PSV a shekara ta 2004 amma saboda wasu dalilai sai a shekara ta 2007 ya koma taka leda a Ingila.

Chelsea na gabda kulla yarjejeniya da makwafin Alex wato Gary Cahill na Bolton.