Rivaldo ya koma taka leda a Angola

rivaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rivaldo

Tsohon shahararren dan kwallo Brazil Rivaldo ya koma kungiyar Kabuscorp ta Angola a wani abu mai ban mamaki.

Tsohon dan wasan Barcelona wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2002 ya sanya hannu a kwangilar shekara daya da kulob din.

Tun lokacin daya bar AC Milan a shekara ta 2004, Rivaldo ya koma taka leda ne a Brazil amma kuma ya dan je kasashen Girka da Uzbekistan yayi kwallo.

A ranar Juma'a ne aka bayyana dan kwallon mai shekaru 39 a gaban manema labarai a birnin Luanda.

Kamar Brazil, a kasar Angola ma ana amfani ne da harshen Portuguese.

Rivaldo shine gwarzon dan kwallon duniya na shekarar 1999.

Kungiyar Kabuscorp tana neman lashe kofinta na farko a gasar kwallon Angola bayan da ta zama na biyu a kakar wasan data wuce.