Anelka ya jinjinawa magoya bayan Chelsea

anelka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nicolas Anelka ya koma kwallo a China

Nicolas Anelka ya fidda wata sanarwa inda yayi godiya ga magoya bayan Chelsea saboda goyon bayan da suka nuna masa a shekaru hudun daya shafe a kulob din.

Dan shekaru talatin da biyu, Anelka ya koma kungiyar Shanghai Shenhuwa ta China inda ya bar turai bayan ya taka leda a kungiyoyi kamarsu Paris Saint-Germain da Arsenal da Real Madrid da Liverpool da kuma Fenerbahce.

Ya lashe gasar premier tare da Arsenal da Chelsea, sai kuma kofin gasar zakarun Turai tare da Real Madrid da kuma gasar kasashen Turai tare da Faransa.

A kakar wasa ta 2008 zuwa 2009, Anelka ne dan kwallon da yafi kowanne zira kwallo a gasar Premier ta Ingila.

Anelka a sanarwar yace"Ina son in yi godiya ga kowa saboda gudun muwar da aka yi mini".