Takaddama kan filin wasan kwallon hannu

Takaddama kan filin wasan kwallon hannu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gasar kwallon hannu na daga cikin wasannin da za a fafata a gasar ta Olympics

Shugaban hukumar kula da kwallon hannu ta Burtaniya Paul Goodwin ya soki matakin da aka dauka na sauya sunan filin wasan kwallon hannu da za a gudanar da gasar Olympics a ciki.

Sabon sunan da aka sanya wa filin na wasu kayayyaki ne da aka yi amfani da su a wajen filin wasan mai daukar 'yan kallo 7,000.

Sai dai hukumar kula da kwallon hannu ta Burtaniya na fafutukar ganin an mayarwa da filin wasan sunansa na asali wato Handball Arena.

"Gasar Olympics ta taimakawa kwallon hannu wurin bunkasa, kuma dukkan alamu na nuna cewa muna samun nasara ta wannan fanni.

"Ina ganin mun cancanci mahukunta su yabawa dukkan kokarin da muke yi wajen inganta gasar, ba wai a baiwa filin wasan wani suna na gama-gari ba wanda ba shi da alaka da kwallon kanta," a cewarsa.

Goodwin ya kara da cewa: "Mai ya sa basu sauya sunan sauran filayen wasanninba kamar yadda suka yi wa wannan?

A Turai baki daya, kwallon hannu ita ce ta fi kowacce farin jini tsakanin mata a Turai, sannan ta biyu a wurin maza, kuma a Burtaniya tana samun daukaka.

Tawagar Burtaniya na da wakilci ta bangaren maza da kuma mata a gasar ta Olympics da za a yi bana a London, kuma kimanin yara 60,000 aka gabatarwa da wasan na kwallon hannu bara.

Wasan farko da aka gabatar a filin na Handball Arena shi ne gwajin gasar Olympics da aka yi a watan Nuwamba, inda tawagar 'yan matan Burtaniya suka bayar da mamaki bayan da suka doke zakarun Afrika Angola.

Karin bayani