London 2012: Yiwuwar yaduwar cututtuka

London 2012: Yiwuwar yaduwar cututtuka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kimanin mutane miliyan goma ne za su halarci gasar ta Olympics

Masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa babban taron da zai hada jama'a kamar gasar wasanni ta Olympics da za ayi a London a bana ka iya haifar da yaduwar cututtuka daga sassan duniya da dama.

Sun ce hakan na iya yin illa ga kasar da za ta dauki bakuncin gasar da kuma sauran jama'a idan sun koma kasashensu.

Suka kara da cewa akwai sauran abubuwa da ya kamata a lura da su wurin mu'amalantar mutane da yawa kamar na gasar Olympics.

Wasu jerin rahotanni da aka wallafa a Mujalllar kiwon lafiya ta The Lancet, sun yi nuni ga illlar hakan.

Bayanai sun nuna cewa haduwar mutane da dama a wuri guda, na kara hadarin yaduwar cututtuka.

Farfesa Ibrahim Abubakar, na jami'ar East Anglia, ya ce akwai hadarin kamuwa da cututtuka a kasa mai masaukin baki da kuma kasashen da 'yan wasan za su fito.

Ya bayar da misali ga tarurruka irin na addini da bukukuwa da wasanni, kamar barkewar cutar 'mura' a wurin bikin tunawa da ranar matasa ta duniya a Australia a shekarar 2008.

Wani rahoto ya bayyana cewa karuwar tafiye-tafiye ta jirgin sama da yaduwar cututtuka za su iya "mummunar illa ga tsarin lafiya, tsaro da kuma al'amuran tattalin arziki a sassan duniya".

"Ana alakanta haduwar jama'a da mutuwa da kuma cunkoso, rushewar gine-gine, tashin hankali tsakanin 'yan kallo da kuma yin illa ga gine-ginen siyasa da na kasuwanci," a cewar Farfesa Brian McCloskey wanda ke kula da harkokin lafiya a gasar ta London 2012.

Karin bayani