Ayila ya ji rauni ba zai je Spain horo ba

ayil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yusuf Ayila

Dan Najeriya Yusuf Ayila wanda ke taka leda tare da Dynamo Kiev a Ukraine ya ji rauni a gwiwarsa ta dama a ranar Litinin.

Wannan raunin dai ya janyo Ayila bai shiga sawun sauran 'yan wasan Dynamo din da zasu je kasar Spain don yin horo na musamman na tsawon makwanni biyu.

Rahotanni sun nuna cewar dan wasan Najeriya din zai samu hutu saboda ya murmure kafin a koma gasar kwallon kasar Ukraine.

Ana saran dai Ayila mai shekaru ashirn da bakwai zai hade da sauran tawagar kulob din a ranar daya ga watan Fabarairu.

Sai dai sauran 'yan Najeriya dake kulob din wato Brown Ideye da Lukman Haruna suna cikin tawagar 'yan kwallo talatin da suka tafi horon a Spain.