QPR na gabda sayen dan Brazil Henrique

henrique Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan Brazil Henrique

Queens Park Rangers ta amince tsakaninta da kungiyar Sao Paulo akan sayen dan Brazil Henrique amma yana bukatar takardar izinin aiki a Ingila.

Dan wasan mai shekaru ashirin ya tattauna da sabon kocin QPR Mark Hughes akan kwangilar wucin gadi ta shekara daya da rabi, tare da damar kulla yarjejeniya ta dundundun.

Henrique wanda ya haskaka matuka a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasada shekaru 20, ya bayyana cewar dama ce me kyau gare shi.

Ya kara da cewar "Kungiyoyi da dama sun nuna sha'awa akai na, amma dana tattauna da Mark Hughes da QPR sai na yanke shawara".

Hughes ya sha kashi a wajen Newcastle a wasansa na farko a QPR, sannan kulob din na zawarcin da Blackburn Chris Samba da kuma dan Chelsea Alex.