Boateng zai yi jinyar wata daya

Kevin-Prince Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin-Prince Boateng

Dan wasan AC Milan Kevin-Prince Boateng yaji rauni, abinda zai sa shi yayi jinyar wata guda.

Koda yake dai Boateng bai shiga cikin tawagar Ghana zuwa gasar cin kofin kwallon Afrika ba, amma dai dole ne yayi hutun wata guda.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce shima golan Milan Christian Abbiati zai yi jinyar mako guda saboda rauni a kafarsa.

Tuni da Milan ta gaggauta maye gurbin Boateng ta hanyar sayen matashin dan wasan Jamus Alexander Merkel daga Genoa.

Merkel mai shekaru 19 dama yana cikin yarjejeniyar musaya tsakanin Genoa da Milan akan Boateng.