Newcastle ta sayi dan Senegal Cisse

cisse Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Papiss Demba Cisse

Dan kwallon Senegal Papiss Demba Cisse ya koma Newcastle United daga kungiyar Freiburg ta Jamus a kwangilar shekaru biyar da rabi.

Dan wasan mai shekaru ashirin da shida ya tafi ya bugawa kasarsa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika inda zai hade Demba Ba.

Cisse ya zira kwallaye tara a cikin wasanni 15, zai saka rigar kwallo mai lamba tara a Newcastle.

Yace"Babban abune in bugawa wannan kulob din".

Koda yake Cisse an kwatanta kimarsa akan fan miliyon 14 amma ana tunanin cewar Newcastle ta bada fan miliyon 10 don samun wanda zai maye gurbin Andy Carroll wanda ya koma Liverpool akan fan miliyon 35 a watan Junairun 2011.