A nada Coleman a matsayin kocin Wales

Chris Coleman Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chris Coleman

An nada Chris Coleman a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallon Wales.

Hukumar kwallon kasar Wales ta kira taron manema labarai a Cardiff don tabbatar da nadinshi a matsayin magajin Gary Speed.

Tsohon dan kwallon bayan Wales, Coleman mai shekaru 41, ya tattauna da mahukunta kwallon kafa na Wales a wannan makon bayan ya bayyana aniyarsa ta maye gurbin Gary Speed.

Coleman yace "Kowane koci yanason ya jagoranci 'yan kwallon kasarsa".

Tsohon kocin Fulham din ya ce mahukunta kwallon kasar ne suka tuntubeshi bayan ya ajiye aikansa a kungiyar Larissa ta Girka saboda matsalolin kudi.