Za a soma gasar kwallon Afrika ranar Asabar

can Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gasar kwallon kasashen Afrika

A karshen wannan makon ne za a soma gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika, inda za ayi wasan farko a Bata tsakanin mai masaukin baki Equatorial Guinea da kuma tawagar Libya wacce ke son nuna cewar an bude sabon babi a kasarta.

Equatorial Guinea na daga cikin kasashe marasa karfi a gasar kuma ta samu gurbin zuwa gasar ne saboda daukar bakuncin hadin gwiwa tsakaninta da Gabon.

Libya ta bada mamakin tsallakewa saboda ta tashi babu ci tsakaninta da Zambia, inda aka zabe ta a matsayin daya daga cikin kasashen da suka tsallake sakamakon rawar da suka taka na share fage.

Wannan dai sabon babi ne ga tawagar Libya wacce ta sauya rigar kwallonta daga kore zuwa fari da ja kuma aka sauyawa tawagar suna zuwa Mediterranean Knights.

An fuskanci kalubale mai yawa wajen shirya wannan gasar ta cin kofin kwallon kasashen Afrika, duk da cewar Equatorial Guinea da Gabon makwabta ne amma kuma suna da bambamci wajen al'adu da yanayi na siyasa.

Equatorial Guinea na karkashin jagorancin daya daga cikin shugabannin Afrika da suka fi dadewa a nahiyar Theodoro Obiang sannan kuma tattalin arzikin kasar na bunkasa saboda man fetur amma kasar na fuskantar matsin lamba akan batun kare hakkin bil adama da kuma 'yancin fadar albarkacin baki.

A Gabon, Shugaba Ali Bongo ya kara kankane mulkin kasar bayan da jam'iyarsa ta samu rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar a watan Disambar bara duk da cewa wasu jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben.

A hukumance ana amfani da harshen Faransanci ne a Gabon a yayinda ake amfani da harshen Spaniyanci a Equatorial Guinea. Wata sarkakiya ita ce ta nisa tsakanin biranen da za ayi gasar a cikinsu, domin babban birnin Equatorial Guinea Malabo na kan tsibirin Bioko kusa da gabar tekun Kamaru.

Kafafen yada labarai dake shirin dauko bayanai a gasar cin kofin Afrika suna fuskantar tsaiko saboda matsaloli wajen neman takardar izinin shiga kasashen biyu. Akwai damuwa matuka akan kasashen biyu da ke bada fifiko akan tsaron kasarsu a yayinda daruruwan masu watsa labarai za su je kasashen.

Masoya wasan kwallon kafa a Afrika na son wasan kamar yadda yake a sauran kasashen duniya amma kuma akwai kalubale matuka akan tafiya daga Zambia zuwa Bata.

Matsalolin da ake fuskanta suna raguwa matuka kuma ana sa ran kasashen Gabon da Equatorial Guinea za su bada mamaki.

Ana saran cewar kasashen Nijer da Botswana wadanda suke halartar gasar a karon farko zasu nunawa duniya kwarewarsu.

Nijer dai zata iya bada mamaki ganin cewar makwabciyarta Najeriya bata tsallake ba, amma kuma Nijer din zata fuskanci kalubale daga wajen Gabon da Tunisia da kuma Morocco.

Tabbas, yawancin abinda ake magana akai shine bayaga Najeriya, akwai wasu manyan kasashe a fagen kwallon Afrika kamarsu Afrika ta Kudu , Masar da kuma Kamaru wadanda ba tsallake ba zuwa wannan gasar. Kuma abin tambaya anan shine, wani irin tasir rashin halartar tasu zai yi ga irin yadda za a murza leda a gasar?

To gannin cewar babu giwayen Afrika da zasu fafata, hanyar ta kasance a bude ga wasu kasashen su nuna kansu. Da dama na ganin cewar Ivory Coast ce zata lashe gasar amma kuma Ghana da Senegal zasu iya bada mamaki. Kuma kasancewar Masar ba zat buga gasar ba, kasashen yankin Arewacin Afrika da za a sawa ido sune Morocco da Tunisia.