QPR na gabda sayen Onuoha daga City

Nedum Onuoha
Image caption Nedum Onuoha

Queens Park Rangers ta amince akan kudin da zata sayi dan wasan Manchester City Nedum Onuoha.

Dan shekaru ashirin da biyar, Onuoha yana samun damar taka leda a lokacin da Mark Hughes yake kocin City.

Amma a kakar wasa ta bana, wasanni uku kacal ya bugawa jagorar gasar Premier.

Onuoha ya soma daga matakin matasa kuma ya ci kwallaye shida a cikin wasanni 100 daya bugawa City amma a kakar wasan data wuce a badashi aro a Sunderland.

Dan wasan wanda haifaffen Najeriya ne ya bugawa City wasan farko a watan Okotobar 2004 a wasan gasar Carling tsakaninsu da Arsenal.

Onuoha ya bugawa Ingila a matakin 'yan kasada shekaru 20.