PSG zata tattauna da City akan Tevez

tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Tevez

Wakilin Carlos Tevez zai tattauna da wakilan kungiyar Paris Saint-Germain ta Faransa akan yiwuwar cefanar da dan kwallon.

Kia Joorabchian zai gana da darektan wasanni a PSG Leonardo akan batun.

Kungiyar wacce a halin yanzu itace ta farko akan teburin gasar kwallon Faransa, tana da kudade masu yawa tun lokacin da wani kamfanin kasar Qatar ya sayi kulob din a bara.

A farkon wannan makonne, Inter Milan ta bada tayin Euro miliyon ashirin da biyar akan dan kwallon Argentina din amma sai Manchester City taki yarda da tayin.

Har wa yau a makon daya wuce ne AC Milan ta janye daga tattaunawa akan sayen Tevez bayan da dan Brazil Alexandre Pato ya ce ba zai koma PSG ba.

A makon daya gabata kuma shugaban Inter Milan Massimo Moratti ya ce"Akwai wasu kungiyoyin dake zawarcin Tevez".

Karin bayani