United ta doke Arsenal da ci biyu da daya

Nasarar Man U kan Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nasarar Man U kan Arsenal

Kwallon da Danny Welbeck ya zura a ragar Arsenal ana gab da hura usur din tashi daga wasan ne ya sanya Manchester United take hango Manchester City wadda ke gabanta da maki ukku a halin yanzu.

Bayan fara wasan ba tare da armashi ba, Antonio Valencia ya ci wa United da ka.

Arsenal ta dan yunkuro bayan hutun rabin lokaci inda Robin van Persie ya jefa kwallon da ta farke cin United.

To saidai da alamu United da gaske take inda Welbeck ya sake zura kwallo ta karshe a ragar Arsenal a wasan.

Yanzu dai Arsenal ce ta biyar a gasar Premier yayinda United kuma ke a matsayinta na biyu.