Chelsea na tattaunawa da Kevin de Bruyne

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Genk da Chelsea ke zawarci, Kevin de Bruyne

Chelsea ta fara tattaunawa da kungiyar Genk ta kasar Belgium domin siyan dan wasan tsakiyar kungiyar Kevin de Bruyne.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 20, ya taso ne a kungiyar, kuma ya buga a tawagar farkon kungiyar a shekarar 2009 sannan kuma ya fara bugawa kasarsa a shekarar 2010.

Kungiyar ta bayyana cewa direktan ta Dirk Degraen ya garzaya Landan domin tattaunawa a kan yarjejeniyar siyan dan wasan.

"Ina ganin za'a kammala tattaunawar a cikin makon nan," In ji mai magana da yawun kungiyar.

De Bruyne ya zura kwallaye biyar a kakar wasan bara da Kungiyar shi ta lashe gasar Belgium.